Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ministan harkokin wajen na Iran Hussain Amir Abdullahiyan ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da takwaransa na kasar China Wang Yi a jiya Laraba.
Ministan harkokin wajen na Iran ya yi ishara da cigaban da aka samu a yayin tattaunawar, sai dai ya ce da akwai wasu muhimman batutuwa da suka saura da ba a kai ga warware su ba.
Amir Abdullahiyan ya kuma ce; Iran ta gabatar da wasu shawarwari aka hanyoyin da za a warware batutuwan da suka saura.
Shi kuwa ministan harkokin wajen na kasar China Wang Yi ya nuna fahimtarsa akan damuwar da Iran take da ita akan batutuwan da suka saura, sannan kuma ya kara da cewa; Idan aka cigaba da tattaunawar kamar yadda take tafiya a yanzu, to za a kai ga warware su.
342/